Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NIJAR: Dubban Dalibai Suka Halarci Jana'izar Dalibin da Ya Rasa Ransa Makon Jiya


Dubban dalibai da mazauna Yamai suka halarci janaizar Mala Bagale dalibin da ya rasa ransa a zanga zangar dalibai makon jiya

Dubban dalibai da mazauna birnin Yamai ne suka yiwa marigayi Mala Bagale, dalibin da ya rasa ransa a zanga zagar dalibai makon jiya, rakiya zuwa makwancinsa na karshe bayan da aka dauko gawarsa daga babban asibitin kasar Nijar zuwa makabartar Yantala yau Litinin.

Duk wanda ya halarci jana'izar ya nuna bacin rai a fili saboda yanayin da dalibin Mala Bagale ya hadu da ajalinsa.

Sakatare janar na kungiyar daliban kasar Nijar Useni Sambo yace 'yan makarantar Nijar gaba daya dake cikin jihar Yamai da duk jama'ar kasar suna cikin takaici da bakin ciki da kunci saboda sun kawo dan uwansu wurin kwanciyarshi na karshe.

Injishi gobe zasu kai wasikar shirin yin jerin gwano cikin makonni masu zuwa saboda su gayawa Shugaban kasa ya kai ta'aziyarsa zuwa ga iyayen Mala Bagale.

Jin takaicin abun da ya samu dalibin sanadiyar samamen da 'yansanda suka kai Jami'ar Abdulmummuni da sunan murkushe zanga zanga ya sa shugabannin kungiyar dalibai ficewa daga zauren taron sulhu da wakilan gwamnati a karkashin Firayim Minista Birje Rafini da sa idon shugabannin addinai da na hukumar kare hakkin dan'Adam jiya da dare.

Bayan sun fito daga dakin taron Nasiru Munkaila na kungiyar dalibai yace manyan jami'an gwamnati da suka bada umurnin a kai samame a Jami'ar suna bukatan a fitar dasu daga mukamansu saboda a cewarsa sun yiwa kasar aikin asha. Yace kawo irin wadannan mutanen a ce su tattauna dasu suna ganin ba'a yi masu adalci ba, ba'a kuma girmama dalibin da aka kashe ba.

Firayim Ministan Nijar Birje Rafini na ganin ficewar shugabannin daliban ba zai hana fahimtar juna ba nan gaba. Yace sai a hankali, ana yi sannu sannu kafin a daidaita.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG