Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'Yan Bindiga Sun Kashe Jami'an Tsaro A Gube


Ma'aikata a Nijar

A cikin daren jiya litinin ne wasu yan bindigar da ba’a san ko su waye ba suka afka wa tashar jami’an tsaro na musamman wanda aka fi sani da jandarma a kauyen Gube da ke Nijar, har suka hallaka jandarmomin uku.

Wani mazaunin kauyen ya yi wa Muryar Amurka bayani ta wayar tarho inda ya ce da kimanin karfe tara na dare aka kai harin, kuma sun ji karar bindiga, har ya shaida cewa an samu mutuwar jami’ai uku. Amman ba a samu mutuwar farar hula ko guda ba.

Hukumomin tsaro a Yamai sun tabbatar da faruwar wannan hari sannan sun tabbatar da mutuwar jandarmomi 3 daga cikin 6 dake aiki a cikin ofishin kauyen na Gube. A halin yanzu ‘yan kauyen su na cikin tashin hankali da zaman dar-dar.

Harin ya zo ne bayan da wata majiyar hukumomin tsaron Nijar ta sanar cewa dakarun kasar sun yi nasarar hallaka 'yan ta’adda sama da 20 a wani gagarimun farmaki da suka kai a yankin Tilleberi a makon jiya, yayin da aka taso keyar 19 zuwa Yamai a yanzu haka. Yankunan Tilleberi da Tahoua masu makwaftaka da Mali da yankin Diffa mai makwaftaka da jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya su ne yankunan da ke fama da hare haren ta’addanci a Nijar, dalili kenan da ya sa gwamnatin ta kafa dokar ta baci a wadannan yankuna yayin da wasu kasashen yammaci suka girke dakaru a wasu sassan na Nijar da nufin bayar da horo da samar da bayanan sirri sai dai duk da haka yan ta’adda kan yi nasarar shiga kasar domin kai farmaki jefi-jefi.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG