Accessibility links

Nijar-Nada Seini Umaru Wakilin Shugaba Isuhu Muhammadu, Ya Sabawa Doka?

  • Aliyu Imam

President Mahamadou Issoufou

Yanzu wannan batu shine ya mamaye kafofin sada zumunta da wuraren hira a zaman batu na muhawara.

Shugaba Muhammadu Isuhu na Nijar, ya nada shugaban jam'iyyar MNSD Nasara a zaman wakilin shugaban kasa. Wannan nadin, yasa masu sharhi suna ganin kamar ba zai rasa nasaba da amsa gayyatar da shugaban na Nijar ya yiwa 'yan hamayya cewa, su taho a kafa gwamnatin hada kan kasa ba.

Yanzu nadin ya janyo muhawara ta ko ina a fadin kasar musamman a dandalin sada zumunta.

Wasu 'yan kasar da suka tofa albarkacin bakinsu kan wannan batu, sunce sam- sam wannan mataki ba shine zai warware dumbin bukatun al'umar kasa ba, wadanda suka hada da kuncin rayuwa da dai sauransu.

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG