Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Sallah Ta Karato, Ba Kudi Ga Tsadar kayayyaki.


Shugaban kasar Nijar Muhammadu Isouffe

'Yan kasa da 'yan kasuwa duk suna kukan hali da ake ciki.

Kasa da mako daya kafin karamar Sallar, 'yan kasuwa da jama'ar gari duka suna kukan rashin kudi. A gefe daya, jama'a suna cewa kayan abinci dana sutura duk sun yi tsada.

Wasu mata da suka je kasuwa sun gayawa wakilin sashen Hausa Haruna Mammane Bako cewa, lamarin ba'a cewa komi. Malama Fatsuma, ta gayawa wakilin Sashen Hausa cewa jama'a suna da kudi, sai dai kayayyaki ne suka yi tsada. Amma wani malamin cewa yayi gaskiyar magana itace, babu kudi.

Suma wasu 'yan kasuwa Abubakar da Habu, suna cewa su dai hali irin na bana daban yake. Suka ce, mutane zasu je rumfunansu su tambayi farashin kaya, amma maimakon su saya, sai su ce sai sun dawo.

Wannan matsala inji wakilin Sashen Hausa Haruna, ba zai rasa nasaba da matsalolin faduwar farashin man fetur, da kuma na wasu ma'adinai kamar Uranium a kasuwannin duniya ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:42 0:00

Facebook Forum

Sakataren Gwamnatin kasar Amurka Michael R. Pompeo

Magoya Bayan Trump Sun Afkawa Ginin Majalisun Amurka

Magoya Bayan Shugaba Donald Trump Sun Mamaye Ginin Majalisar Dokokin Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:56 0:00

Rayuwar Birni

Rayuwar Birni: Hira da Aliyu Danlami mai sayar da furanni a Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:49 0:00
Karin bayani akan Rayuwar Birni
XS
SM
MD
LG