Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Ta Bi Sahun Kasashen Duniya da Tunawa da Yau A Matsayin Ranar Cutar Kanjamao


Halaru Shaibu na ma'aikatar kiwon lafiyar kasar Nijar
Halaru Shaibu na ma'aikatar kiwon lafiyar kasar Nijar

Yau ranar talatin ga watan Nuwamba ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ko MDD ta kebe kowace shekara domin tunawa da kuma fadakar da jama'a akan cutar kanjamao ko sida

Jamhuriyar Nijar ta bi sahun sauran kasashen duniya domin tunawa da ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe domin yaki da cutar kanjamao ko sida.

Wakiliyar sashen dake kula da cutar kanjamao ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar Nijar ita ce ta gabatar da jawabi ma kafofin yada labarai na gwamnati.

Shugabar tana cewa yau ce ranar da aka kebe domin yaki da cutar sida kuma ana tunawa da mutane miliyan saba'in da takwas dake dauke da kayar cutar a duk fadin duniya. Tace haka ma "muna nuna alhininmu da mutane miliyan talatin da biyar da suka rasa rayukansu sanadiyar wannan cutar tun lokacin da ta bayyana zuwa yau", inji wakiliyar.

Ta cigaba da cewa mutane su sani Majalisar Dinkin Duniya ta dauki alwashin gamawa da wannan cutar nan da zuwa shekarar 2030. Tace "muna samun nasarori da dama daga mutanen da shekarunsu suka manyanta amma cutar ta kara habaka wajen yara mata"

A lokacin da aka tattauna dashi Malam Lawali Shebu wani jami'i mai kula da wayewa al'umma kai game da cutar sida a cikin tashar daukan fasinjoji ta garin birnin Konni yace yana da kyau jama'a su maida hankali game fadakarwar da ake yi masu akan cutar.

Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG