Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Ta Kafa Kwamitin Gyara Dokokin Zaben Kasar


Shugaban Kasar Nijar Mahamadou Issoufou

Kwamitin da ya kunshi mutane goma sha takwas kuma yana da makonni biyu ya kammala aiknsa.

Dokokin da kwamitin zai tantance sun hada da sashe na 48 na kundun tsarin mulkin kasa dake fayyace adadin kwanakin shirya zaben shugaban kasa kafin shudewar wa'adin shugaba mai ci.

Baicin wannan sashen akwai kuma dokokin zabe da suka hada da dokar dake tsara ka'idodin hukumar zabe da dokar da ta shafi zaben 'yan majalisar dokokin kasa da shugaban kasa da na shugabannin kananan hukumomi da na zaben raba gaddama.

Malam Yahaya Garba mai magana da yawun kwamitin yace zaben da ya wuce an lura cewa dokokin zaben kasar suna da kurakurai da ya kamata a gyarasu. Kwamiti dinsu na kwararru ne da ministan cikin gida ya kafa. Cikin makonni biyu zasu duba dokokin.

Shugaban jam'iyyar Model Ma'aikata kuma dan takara a zaben shugaban kasa Alhaji Tahiru Gimba yana cewar akwai wata boyayyar manufa bayan wannan yunkurin na gwamnati. Yace kwamitin da aka kafa na masu mulki ne domin a canza kundun mulki har a kaiga zaben jin ra'ayin jama'a. Yace akwai manufar "ta zarce ciki" Yace suna saurare su ga abun da zai faru amma sun san nufin nada girma sosai.

To saidai kakakin kwamitin kuma bugu da kari sakataren majalisar CNDP Yahaya Garba ya musanta zargin na Alhaji Gimba. Yace cewa aka yi a duba tsarin gudanar da zabe gaba daya amma kuma wasu sun soma rudar mutane suna kawo wasu hujjoji daban. Yace ba kwamitin ne zai yiwa kundun tsarin mulkin ksa kwaskwarima ba.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00
Shiga Kai Tsaye

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG