A jamhuriyar Nijar ‘yan bingida sun halaka shugaban wata makarantar firaimari a jiya alhamis a wani kauyen yankin Tilabery, bayan sun kashe wasu magina 4 a karkarar Anzuru.
Wannan shine dalilin da yasa kungiyoyin malaman kwantaragi kiran hukumomi su dauki matakan kare malamai daga wannan barazana. To sai dai tuni gwamnati ta bayyana shirin daukar matakan da suka dace domin kare rayuwar malaman makaranta a duk inda suke.
Lamarin ya faru ne lokacin da malamin makarantar ke kokarin komawa kauyen da yake aikin malanta bayan da ya dauko kayayyakin karatun yara a daya daga cikin kauyuka makwafta, kamar yadda sakataren kungiyar malaman Synaceb reshen Tilabery Moussa Maman Mahamadou ya shaida.
A Yamai kungiyoyin malaman makaranta sun bayyana damuwarsu game da faruwar wannan al’amari.
Sakataren kungiyar Synafces Jariri Labo ya ce kisan shugaban makarantar kauyen Doukou Makani wani abu ne dake nunin an shiga sabon babi a tashe tashen hankulan da suka addabi yankin Tilabery.
A cewar Mounkaila Halidou yanzu an kai matsayin da zai sa hukumomi su gaggauta daukar matakan kare lafiyar wadanan ma’aikatan kasa.
Ministan ilimi Dr. Daouda Mahamadou Marthe dake ziyara a yanki Diffa ya tabbatar da cewa gwamnati ba za ta yi kasa a guiwa ba wajen baiwa malaman makaranta kariya.
A saurari cikakken rahoto cikin sauti daga Nijar.
Facebook Forum