Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Nijar Tace Zata Kwato 'Yan Kasar Da 'Yan Binidga Suke Garkuwa Dasu.


Shugaban NIjar Muhammadu Isouffe na hudu daga hanun hagu.

A hare haren da 'yan Boko Haram suka kai na baya bayan nan ne suka saci mata da matasa maza 37.

A Nijar, gwamnatin kasar tace ba zata yi kasa a guiwa ba wajen gano ‘yan mata 26 da samari 11 da mayakan Boko Haram suka sace, bayan hare haren da suka kai a Ingilewa a yankin Diffa, a ranakun 2-3 ga watan nan.

Kakakin gwamnatin kasar Asmana Mal Isa ne ya bayyana haka, lokacinda ya bayyana a kafofin yada labaran kasar a daren jiya talata, domin bayyana matsayar gwamnatin kan hare haren da ‘yan binidgar suka kai wanda ya halaka akalla mutane 9.

Wannan hari inji kakakin na gwamnati, yazo ne mako daya bayan wani hari da ‘yan bandigar suka kai a gari da ake kira Kablewa, akan wani sansanin ‘Yan gudun hijira.

A lokacin harin ‘yan kunar bakin wake biyu sun halaka, da wasu mutane biyu. Mutum 11 kuma sun jikkata, hudu daga cikinsu suna cikin mawuyacin hali.

Daga nan gwamnatin ta yi kira ga al’uma su ci gaba da harkokinsu kuma su baiwa jami’an tsaro dukkan hadin kai da suke bukata.

Kakakin na gwamnati ya kuma mika ta’aziyyar gwamnati da jami’anta ga iyalan wadanda hare haren suka rutsa da ‘yan uwansu.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00

Facebook Forum

An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Ziyarar Sakatare Blinken A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG