Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijeriya Za ta Sayi Sabbin Jiragen Sama Uku ma Shugaban Kasa


Jirgin Sama Kirar Falcon 7X, Daya daga cikin irin Jiragen da Nijeriya ta ke son saya wa Shugabanta
Jirgin Sama Kirar Falcon 7X, Daya daga cikin irin Jiragen da Nijeriya ta ke son saya wa Shugabanta

Nijeriya ta ce za ta sayi wasu sabbin jiragen sama guda uku kan kudi kimanin Naira Miliyan Dubu Ashirin da biyu wa Shugabanta duk da bukatar kudin da ta ke na wasu ayyuka.

Nijeriya ta ce za ta sayo sabbin jiragen sama kirar jet-jet wa Shugaban kasar, a daidai lokacin da kasar ke kokarin neman kudin fara shirin zabe mai zuwa da kuma farfado da bangaren wutar lantarki.

Ministar Yada Labarai, Madam Dora Akunyili, ta fadi yau Laraba cewa Majalisar Ministoci ta bayar da umurnin sayo jiragen sama samfurin Falcon 7X guda biyu daga kasar Faransa da kuma sanfurin Gulfstream G550 guda daya daga Amurka. Za su lakume wajen dala miliyan 150.

Akunyili ta ce dama an samar da kudin a kasafin kudin 2010 na Nijeriya.

Jiya Talata, Yan Majalisar Tarayyar Nijeriya su ka bada izini a takardance, wanda zai bai wa gwamnati damar aro kudi, don ta hada dala miliyan 585 don shirin babban zaben 2011.

Shugaba Goodluck Jonathan ya kuma yi alkawarin gina sabuwar tashar wutar lantarki da za ta ci dala miliyan dubu 3 da dari biyar don inganta fannin samar da wutar lantarki. Ya ce da gwamnati ne da yan kasuwa da cibiyoyin cinakayya da kawo cigaba na kasa da kasa za su dau nauyin.

XS
SM
MD
LG