Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NOMA TUSHEN ARZIKI: Sanarwar Bayan Taron Makiyaya Da Manoma a Nijar - Afrilu 20, 2021


Mohammed Baballe

A karshen wani taron da suka gudanar a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar, kwararu da jami’an kare hakkin manoma da makiyaya sun kudiri aniyar tunkarar matsalar satar irin shukoki da na dabobi da ake fuskanta a ‘yan shekarun nan bayan la’akari da yadda wasu kamfanonin kasa da kasa ke manna tambarinsu a kan irin shuka duk kuwa da cewa abu ne da mazaunan karkara suka gada iyaye da kakanni.

Taron wanda ya sami halartar tawagogin kasashe 7 na CEDEAO da kasar Chadi, ya bada misalin yadda wasu ‘yan Senegal suka yi yunkurin mayar da irin albasar Galmi ta Nijar a matsayin mallakinsu, abin da ke zama wata barazana ga ci gaban ayyukan noma da kiwo a Nahiyar Afrika, kamar yadda za a ji sanarwar karshen taro daga bakin Diori Ibrahim na kungiyar Alternative.

NOMA TUSHEN ARZIKI: Sanarwar Bayan Taron Makiyaya Da Manoma a Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:07:15 0:00


XS
SM
MD
LG