Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NOMA TUSHEN ARZIKI: Yadda Masu Sayar Da Ciyawa Ke Barazanar Batar Da Irin A Yankunan Karkara - Mayu 4, 2021


Mohammed Baballe
Mohammed Baballe

A jamhuriyar Nijar shugabanin kungiyar kare hakkin manoma da makiyayan kasar wato Plate Forme Paysanne sun koka a game da yadda masu sayar da ciyawar dabobi ke barazanar batar da irin ciyawa a yankunan karkara, lamarin da ka iya haifar da koma baya ga sha’anin kiwo yayin da a daya bangare abin ke hanawa manoma samun takin gargajiya.

A cewar shugaban wannan kungiya Malam Djibo Bagna bunkasar kasuwancin ciyawar dabobi a manyan birane ne ya sa masu irin wannan sana’a, kakkabe dukkan albarkatun gonaki ba tare da la’akari da irin illolin da abin ka iya haddasawa ayyukan noma da kiwo ba.

NOMA TUSHEN ARZIKI: Yadda Masu Sayar Da Ciyawa Ke Barazanar Batar Da Irin A Yankunan KarkaraDa
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:25 0:00


XS
SM
MD
LG