Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Obama Zai Ziyarci Masallaci a Karon Farko


Wannan ziyarar zata baiwa shugaba Obama damar isar da sakon na masamman ga al’umar Musulmin

Shugaban Amurka Barack Obama, zai ziyarci wani Masalaci, a birnin Baltimore, ta kasar Amurka a karon farko tun hawarsa karagar mulki.

Wannan ziyarar zata baiwa shugaba Obama damar isar da sakon na masamman ga al’umar Musulmin Amurka cewa zai karewa Musulmi ‘yancinsu na gudanar da harkokinsu na addini da al’adunsu.

Kakakin fadar White House, Josh Earnest, yace shugaba Obama, zai gana da shuwagabanin musulmai a Amurka, domin jin abubuwan dake ci masu tuwo a kwarya.

Musulmi, a Amurka sun jima suna bukatar shugaba Obama, da ya ziyarci Masallaci, irin wannan bukatar na baya bayan nan yazo ne lokacin da manyan jami’an , fadar White House suka gana da wasu shuwagabanin Musulmi, a watan Disambar da ta gabata biyo bayan nuwa kyama ga al’umar Muslumi .

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG