Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Obama Ya Saka Hanu Kan Dokar Zabtare Kudade Da Gwamnati Take Kashewa


Shugaba Obama a fadar White House jiya jumma'a yana magana kan zabtare kudaden da gwamnati take kashewa.
Shugaban Amurka Barack Obama ya sanya hanu kan dokar da zata zabtare dala milyan dubu 85 kai tsaye daga cikin kudade da gwamnati take kashewa, wadda zai fara aiki sabo da majalisar dokokin Amurka da fadar White House sun kasa cimma daidaito kan duba wadansu hanyoyin rage gibi a kasafin kudin Amurka.

Zai dauki makonni kamin a soma jin radadin wannan mataki a duk fadin kasar, amma tuni aka fara jin tankiya kan haka.

Mr. Obama cikin jawabinda yake yi a karshen mako ranar kowace Asabar, yace an dauki wannan mataki ne sabo da wakilan majalisar dokoki ‘yan Republican sun gwammace kare muradun masu hanu d a shuni, maimakon kula da sojoji da mutane wadanda suke tsaka-tsaki a harkar rayuwa.

A jawabin maida martani na jam’iyyar Republican da ‘yar majalisa Cathy McMorris Rodgers daga jihar Washington ta gabatar, tace, akwai yadda za a gudanar da wannan zabtarewar ta hanyoyi masu ma’ana.Tace a maye gurbin zabtarewar da wani shiri da yafi kama hankali.

Tuni wasu hukumomin gwamnati suka dakatarda daukan sabbin ma’aikata da kuma rage kudade da suke kashewa wajen tafiyarda wasu ayyuka domin kaucewa tilastawa ma’aikata daukan hutun dole domin rage kudaden da za a biya su.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG