Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Obama Ya Yi Gargadin Kin Amincewa Da Gaskiya


Obama yayin da ya ke jawabi a bikin cika shekaru 100 na Nelson Mandela a Johannesburg ranar 17 ga watan Yulin 2018.
Obama yayin da ya ke jawabi a bikin cika shekaru 100 na Nelson Mandela a Johannesburg ranar 17 ga watan Yulin 2018.

Obama ya bayyana hakan ne a jiya Talata a birnin Johannesburg, inda yaje domin halartar bikin cika shekaru 100 na shahararren mai yaki da tsarin wariyar launin fata Nelson Mandela da yana raye.


Zuwa wannan biki, shi ne babban taro irinsa na farko da Obama ya halarta, tun bayan da ya sauka daga karagar mulki a bara, bayan da ya kwashe shekaru takwas yana mulki.


“Kin amincewa da gaskiya, dabi’a ce da ta yi hannun babbar riga da tsarin dimokradiyya, dalilin kenan da ya sa ya zama dole mu jajirce wajen kare kafafen yada labarai masu zaman kansu, mu kuma himmatu wajen yaki da dabi’ar mayar da kafafen sada zumunta, dandalin nuna fushi da yada karerayi,” inji Obama

Tsohon shugaban na Amurka, ya kuma yi kira ga masu rajin kare dimokradiyya, da su yi koyi da Mandela, wanda ya jajirce tare da nuna fata na-gari, wajen ganin cewa makarantu suna koyar da matasa “darrusan da suka jibinci yin zurfin tunani a koda yaushe, ba wai kawai su rika yin biyayya, ba tare da sanin makomarsu ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG