Accessibility links

Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo Yace Ya Fidda Hanu A Harkokin PDP.

  • Aliyu Imam

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo.
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo yayi barazanar daga yanzu zai zama dan kallo ne kawai cikin harkokin jam’iyyar PDP mai mulkin Najeriya, muddin ba a yi gyara a yadda ake tafiyarda jam’iyyar ba.

Obasanjo ya bayyana haka ne cikin wata sabuwar wasika da ya rubutawa shugaban jam’iyyar Alhaji Bamanga Tukur da wasu jigajigan jam’iyyar, aka kuma aikewa kafofin yada labarai ciki harda ofishin sashen Hausa dake ikko, daga inda wakilinmu Ladan Ibrahim Ayawa ya aiko mana da rahoto.
XS
SM
MD
LG