Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ofishin Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya Yayi


Ginin hukumar kwallon kafa ta Najeriya yana cin wuta.

Kawo yanzu babu masaniya kan musabbabin tashin wannan gobara.

Ofishin hukumar kwallon kafa ta Najeriya, yayi gobara, da sanyin safiyar yau Laraba.

A jiya ne aka maida Aminu Maigari, a matsayin shugaban hukumar kwallon kafa ta najeriya, bayan da aka ta gai gwauro da mari kan shugabanshi hukumar.

Kawo yanzu babu masaniya kan musabbabin tashin wannan gobara wanda yayi sadiyar rasa naurori da kuma muhimman takardu.

Shugaban hukumar ta kwallon kafar Najeriya, Aminu Maigari, yace a halin yanzu baya zargin kowa, amma yace idan har da hannun wani a dalilin tashin wannan gobaran to tabbaci hakika asiri zai tonu.

Ya kara da cewa jami’an tsaro zasu gano duk abunda ya faru da tabbatar da cewa idan da hannun wani ko kuma wasu duniya zata sani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:30 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG