Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ofishin Jakadancin Amurka Ya Shirya Taron Bita wa 'Yan Jarida da Masu Magana da Yawun Gwamnati


President Donald Trump speaks with members of the armed forces via video conference at his private club, Mar-a-Lago, on Thanksgiving, Nov. 23, 2017, in Palm Beach, Florida.
President Donald Trump speaks with members of the armed forces via video conference at his private club, Mar-a-Lago, on Thanksgiving, Nov. 23, 2017, in Palm Beach, Florida.

Taron na cike gibi ne tsakanin 'yan jarida da masu magana da yawun gwamnati saboda a samu daidaito a rahotannin da zasu dinga yayatawa

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari shi ya bukaci ofishin jakadancin Amurka ya shirya taron bitan wa 'yan jarida da masu magana da yawun gwamnati.

Jakadan Amurka shi ya bude taron a Abuja babban birnin Najeriya wanda na hadin gwiwa ne tsakanin kungiyar 'yan jarida da ofishin jakadancin..

Jakadan yace taron bita da masu magana da yawun gwamnati ka iya zaburar da kungiyoyin waje domin karfafa cudanyarsu da Najeriya.

Yace babban kalubale shi ne yin magana da yawun gwamnati. Wani kalubalen shi ne tabbatar da an isar da sakon da aka so isarwa da kuma halin da bangarori da sauran ma'aikatun gwamnati ke ciki. Yace kamata ya yi masu magana da yawun gwamnati daga bangarori daban daban su san abun da kowane bangare ke ciki ko zai sanar.

Malam Garba Shehu mataimakin daraktan yada labarai na shugaban kasa yace an shirya taron ne saboda duk masu magana da yawun gwamnati sun s an abun da yake faruwa ba tare da cin karo da juna ba. Fadar gwamnati yakamata ta san duk abun da sauran ma'aikatu ke yi. Amma yanzu kowa na yin abun da yaga dama. Taron na kawo gyara ne.

Shi ma shugaban 'yan jaridan Najeriya Alhaji Abdulwahid Odunsunde yace taron domin a cike gibin dake tsakanin 'yan jarida da masu magana da yawun gwanati ne.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:37 0:00

XS
SM
MD
LG