Kungiyar Olando Pirates ta Afrika ta Kudu wacce take kan gaba a rukunin B a gasar cin kofin zakarun Afrika ta hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF a takaice, ta sha kashi a hannun Esperance ta kasar Tunisia a ranar Talata, lamarin da ya sauko da ita daga matsayi na farko a cikin rukunin.
Mai horar da ‘yan wasan Orlando Pirates Milutin Sredojevic, ya yi sauye-suaye tsakanin ‘yan wasan sa, a kan yanda ya yi wasa da Kaizer Chief a karshen mako inda ya raba rana da Kaizer Chief ba kare bin damo.
Ita Esperance mai daukar bakwancin wasan ta mamaye zagayen farkon wasan kuma ta yi nasarar fara zura kwallon farko ta kafar dan wasanta Anice Badri a wani bugun tazara a daidai minti 15 da fara wasan.
Orlando Pirates mai lakabi Buccaneers ta gaza tabuka abin kirki a wasan kuma ta zubar da dama da ta samu wanda zai iya taimaka mata ta dau fansa.
Daga karshe ana saura minti biyu a gama wasa Esperance ta sake zura wani kwallon ta kafar Haythem Jouini da ya kai ta ga samun nasarar ci biyu da babu a kan Orlando Pirates, wacce yanzu ta sauko da saman rukunin B a gasar cin kofin zakarun Afrika ta hukumar CAF.
Facebook Forum