Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Operation A Watse Na Ci Gaba Da Samun Nasara A Wasu Yankunan Jihohin Lagos Da Ogun


Sojojin Najeriya

Duk kokarin da ma’aikatar tsaron Najeriya ke yi na samar da zaman lafiya a wasu garuruwan jihohin Ogun da Lagos, har yanzu ana kai wasu ‘yan hare hare.

Kakakin ma’aikatar tsaron Najeriya Birgediya Janal Rabe Abubakar, shine ya tabbatar da cewa har yanzu ana kai hare haren a wasu yankunan jihahin Ogun da Lagos, a tattaunawarsa da wakilin Muryar Amurka Hassan Umar Tambuwal. Haka kuma ya tabbatar da cewa har yanzu sojoji suna gudanar da aikin tsaro da ake yiwa take da suna Operation A Watse, wanda kuma ke ci gaba da samun nasara.

Yanzu haka dai sojoji na samun nasara a kan ‘yan kungiyar Niger Delta dake yankunan a jihohin Lagos da Ogun, Janal Rabe ya musunta rahotannin dake cewa har yanzu wasu tsagerun dake wadannan yankuna na cin karensu ba babbaka, ya kuma tabbatar da cewa tun lokacin da aka gudanar da Operation A Watse, aka taka musu birki sai dai wasu abubuwa da ba a rasa ba.

Sojojin Najeriya zasu kasance a wannan yanki domin tabbatar da cewa babu wani sauran tashin hankali. Daga karshe Janal Rabe, yayi kira ga al’umomin yankin da su hada kai da jami’an tsaro don tabbatar da cewa bata gari da ‘yan ta’adda basu dawo yankunan ba.

Domin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG