Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Osinbajo Ya Sallami Shugaban Hukumar Tsaro Ta DSS


Mataimakin Shugaba Yemi Osinbajo Switzerland Davos Forum
Mataimakin Shugaba Yemi Osinbajo Switzerland Davos Forum

Mukaddashin Shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya umurci shugaban hukumar tsaron ta farin kaya DSS Lawal Daura ya mika ragamar ofishinsa ga wanda ya ke biye da shi a girman mukami.

Sanarwar mukaddashin shugaban ta zo ne daidai lokacin da jami'an tsaro su ka dauki matakin hana wasu 'yan majalisa shiga majalisar da hasashen barin wasu su shiga don yunkurin tsige Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki.


Duk da sanarwar ba ta danganta lamarin kwabe Lawal Daura da abun da ya faru a majalisa ba, memba a hukumar 'yar sanda Naja'atu Muhammad ta ce matakin haka ya ke nufi kuma ya dace.

A cewarta, shi ya tura jami'an tsaro su ka mamaye majalisa don haka matakin kwabe shi da mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya yi ya yi daidai.

Ta ci gaba da cewa, majalisa ita ce ta bambanta mulkin soja da na dimokradiyya, don haka 'yan majalisar ko da sun kasance dujal, su suke wakiltar mu.


Yanzu dai za a jira a ga yanda 'yan majalisa masu hamayya da juna za su kammala wannan takaddama da ta ke kama da wasan kwaikwayo a yayin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na hutun kwanaki 10 a Landan.

Saurari cikakken rohoton

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:23 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG