Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kome Ya Tsaya A Birnin Karachi Na Pakistan Domin Zaman makoki.


Wani yake wucewa a birnin karachi inda aka tsaida kome saboda zaman makoki.
Wani yake wucewa a birnin karachi inda aka tsaida kome saboda zaman makoki.

An kashe akalla mutane 56 a tarzomar siyasa da ta fara tun ranar Asabar,a birnin na karachi dake kan gaba. Ko ina ka juya cikin birnin Laraban nan sai jami'an tsaro ake gani suna sintiri.

Sakamakon tarzomar siyasa da ta halaka akalla mutane 56 da aka fara tun ranar Asabar, yau birnin Karachi dake kan gaba an tsaida kome domin zaman makoki.

Yau laraba, ta ko ina ka juya cikin birnin, jami’an tsaro ne suke sintiri,‘yan kansuwa basu fita ba,san nan an tsaida aikin motocin diban fasinja a galibin sassan birnin.

PM Pakistan Yousuf Reza Gailani, yace gwamnati bata yanke shawarar tura sojoji ba saboda hukumomin farin kaya zasu iya magance lamarin ahalin yanzu. Jami’ai suka ce akalla mutane 55 ne suke hanu danagane da wan nan fitina.

A daya daga cikin harin mafi muni a lokaci daya ‘yan bindiga dadi suka kashe mutane 11 cikin wata kasuwa jiya talata.

Tarzomar ta zo a dai dai lokacinda ake zaben cike gurbin kujerar wani dan majaisa ranar lahadi,wanda aka kashe a farkon bana.

Jam’iyyar MQM wacce take wakiltar al’umar Urdu masu rinjaye da abokiyar hamayyarta ANP suna zargin juna da janyo wan nan tashe tashen hankula.

XS
SM
MD
LG