Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Ta Nuna Alamun Goyon Bayan Nouri Al-Maliki A Dambarwar Siyasar Iraqi


Firayim minista Nouri al-Maliki na Iraqi (hagu) yana tattaunawa da shugaba Mahmoud Ahmadinejad na Iran (dama), litinin 18 Oktoba 2010 a birnin Teheran. Tafinta ne ke zaune a tsakiyarsu.

Amurka ta koka kan cewa ya kamata Iran ta daina yin katsalanda a harkokin siyasar Iraqi, ta zamo makwabciyar kwarai ta hanyar mutunta diyaucin Iraqi

Iran ta nuna alama mafi karfi ta goyon bayan firayim minista Nouri al-Maliki na Iraqi domin ya jagoranci kasarsa a wa’adi na biyu, abinda ya sa Amurka ta koka game da katsalanda da ta ce Iran tana yi a harkokin siyasar Iraqi.

Sa’o’i a bayan da al-Maliki ya isa Teheran jiya litinin, mukaddashin ministan harkokin wajen Iran, Rauf Sheibani, yace firayim ministan yana daya daga cikin wadanda suka dace su jagoranci gwamnatin Iraqi ta gaba. Kamfanin dillancin labaran Iran na IRNA, ya ambaci Sheibani yana misali da gogewar al-Maliki wajen jagorancin Iraqi, yana kuma nuni da hali mai sarkakiya da kasar ta shiga a saboda janye sojojin Amurka da ake yi daga can.

Daga bisani, shugaban addini na Iran, Ayatollah Ali Khameini ya fadawa al-Maliki cewa ya kamata Iraqi ta kafa tsaro da kuma sabuwar gwamnati ba tare da jinkiri ba. Shugaban addinin bai fito a fili yace yana goyon bayan al-Maliki ba.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bukaci shugabannin Iraqi da su yi taka tsan-tsan, tana mai fadin cewa Iran tana iya zamowa makwabciyar kwarai ta hanyar mutunta diyaucin Iraqi tare da kawo karshen goyon bayan masu amfani da tashin hankali a cikin Iraqi.

XS
SM
MD
LG