Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Papa Roma yace Donald Trump ba Kirista ba ne


Papa Roma Francis

Papa Roma ya tsunduma cikin siyasar Amurka inda ya yi shakkar ko Donald Trump dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar Republican Kirista ne soboda kiyayya da dan takaran yake nunawa baki da ba Amurkawa ba musamman 'yan Mexico da Afirka

Yau Alhamis, Papa Roma Francis, ya tsoma kansa cikin siyasar Amurka, inda yayi nuni da cewa mutumin da yake kan gaba a jerin masu takara shugabanci watau Donald Trump ba "Kirista ba ne", saboda shawarar da ya bayar na gina babbar ganuwa kan iyakar Amurka da Mexico ta kudancinta domin hana bakin haure tsallakowa cikin Amurka.

Shugaban darikar katholikan yayi wannan furucin ne kan hanyarsa ta komawa Roma bayan ziyarar da ya kawo Mexico cikin makon nan, har ya jagoranci addu'a ta musamman abainar dubban jama'a jiya Laraba, kusa da kan iyaka da jihar Texas, zangon galibin bakin haure masu zuwa daga Mexico da sauran kasashe dake Latin Amurka.

Trump wanda dan darikar Presbitarian ne wanda yake yakin neman zabe a jihar Carolina ta kudu, yace kalaman Papa Roman ba "kalamai ne da suka dace ba."

Yace "shakkun da Papa Roma ya nuna kan addininsa abun takaici ne"

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG