Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PDP: Kwamitin Riko Zai Tattauna Yiwuwar ‘Daukaka ‘Kara a Kotun Koli


ABUJA: Taro PDP bangaren Sanata Ahmadu Makarfi
ABUJA: Taro PDP bangaren Sanata Ahmadu Makarfi

Yau Litinin kwamitin riko na jam’iyyar PDP zai yi zama don tunanin yiwuwar ‘daukaka ‘kara zuwa kotun ‘koli kan hukuncin da kotun Fatakwal ta yanke na baiwa Sanata Shariff shugabancin jam’iyyar.

Kama daga ‘yan Majalisa da tsoffin Gwamnoni da Ministoci na jam’iyyar PDP na nuna goyon baya ga kwamitin riko na jam’iyyar karkashin Sanata Ahmed Makarfi, da kotun ‘daukaka ‘kara ta sauke daga mukami ta hanyar haramta taron da ya ‘daura kwamitin kan aiki da tabbatarwa Ali Modu Shariff hakkin shugabancin jam’iyyar.

Sai dai kuma wasu jigogin PDP irin su mataimakin tsohon shugaba Jonathan kan Majalisa, Cairo Ojougboh da tsohon mai taimaka masa kan siyasa Ahmed Gulak, da ‘dan kasuwa Jima Ibrahim, baki ‘daya suna mubayi’a ga Sanata Ali Modu Shariff.

Zuwa yanzu dai Sanata Shariff, na ci gaba da jan ragamar jam’iyyar daga ofishin wucin gadi dake Maitama Abuja. Ya yinda kwamitin Makarfi ke aiki daga wani ofishi a Wuse, inda a yau Litinin kwamitin zai yi zama don neman hanyar ‘daukaka ‘kara a kotun koli.

A cewar Sanata Sheriff, “Abin da ya faru tamkar bude sabon babi ne na abubuwan alheri da zasu sami PDP,” inji Sanata Sheriff, wanda ke bukatar sauran ‘yan jam’iyyar su zo su hada kai da shi, don shirya babban taron zaben sabbin shugabanni, maimakon bugewa da zuwa kotu.

Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya daga Abuja.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG