Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PDP Ta Ce Ta Ja Daga


Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Atiku Abubakar, jigo a jam'iyyar PDP

Babbar jam'iyyar Adawa ta PDP, wadda kwanan nan tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya sake komawa ciknta, ta yi babban taro inda ta samu sabon jagoranci tare da shan alwashin cewa za ta yi galaba a zabe na gaba.

Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya PDP ta ce ta karce kasa a siyasance kuma zabe mai zuwa za ta ba da mamaki. Jam’iyyar ta yi wannan ikirarin ne a yayin babban taronta wanda ya haifar da sabon shugabanci.

Da ya ke mika shugabancin jam’iyyar a hukumance ga sabon shugaban jam’iyyar na kasa Prince Uche Secondus, tsohon shugaban na riko Sanata Ahmed Muhammed Makarfi ya ce ya karbi shugabancin nakasasshiyar jam’iyya, to amma ya mika kakkarfar jam’iyya ga sabon shugabanta.

Kan ko shin an yi taron na PDP da kuma yin sabbin shugabanni bisa ka’ida, wani lauya mai zaman kansa da ke Abuja mai suna Barrister Abubakar Kurawa ya ce a shari’ance ana iya cewa PDP ta yi daidai, to amma a siyasance da alamar ayar tambaya. To amma sai ya kara da cewa abu mafi muhimmanci shi ne jam’iyyar ba ta saba ma doka ba.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:02:30 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG