Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PDP Ta Dare Gida Biyu Saboda Rikicin Kujerar Ciyaman


Alama
Alama

Rigimar cikin gidan jam'iyyar PDP ya fa dau wani sabon salo, bayan da wani jigon jam'iyyar daga arewa maso gabashin kasar ya mamaye Sakatariyar jam'iyyar ya ayyana kansa a matsayin sabon Ciyaman.

Rikicin Shugabancin babbar jam’iyyar adawa ta PDP ya dau sabon salo, bayan da tsohon Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara Kan Siyasa Ahmed Gulak ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban jam’iyyar, ganin kotu ta zartas cewa yankin arewa maso gabas ne ya kamata ya fitar da ciyaman din jam’iyyar.

Wannan matakin da Gulak ya dauka ya kai ga rabuwar jam’iyyar gida biyu, wato da bangaren Ciyaman din da Gulak ya ce ya maye gurbinsa wato Uche Secondus da kuma bangaren shi Gulak din. Dama Gulak ya kai kara ne kan cewa kamata ya yid an arewa maso gabashi ya gaji Ahmed Mu’azuz amma bad an yankin da Secondus ya fito ba.

To saidai Mataimakin Sakataren Labaran PDP Abdullahi Jalo ya ce ba Gulak ne kadai ya dace ya gaji Ahmed Mu’azu ba; Shi kansa Jalon na daya daga cikin wadanda su ka cancanci yin takara. Don haka ya rage gwamnoni da sauran manyan ‘yan jam’iyya su zauna su yanke shawara.

Ga wakilinmu Nasiru Adamu Elhikaya da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG