Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

PLATEAU: Al’ummar Irigwe a Karamar Hukumar Bassa Ta Kira Gwamnatin Tarayya Ta Binciki Kashe-kashen Yankinsu


Gwamnan Jihar Filato Mr. Simon Lalon

Wani rikicin da ya barke a Jabu Miyango dake karamar hukumar Bassa tsakanin wasu ‘yan bindiga da kabilar Irigwe, ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a yankin, lamarin da ya sa al’ummar kiran gwamnatin tarayya ta gudanar da bincike

Al’ummar Irigwe dake karamar hukumar Bassa a jihar Filato sun bukaci gwamnatin tarayyar Najeriya da ta gudanar da bincike kan kashe-kashen dake aukuwa a yankin da zummar gano masu laifi domin a hukumtasu.

Taron manema labarai da Kungiyar Raya Al’adun Irigwe ta kira, ya biyo ne bayan kisan wasu mata da yara 29 da wasu ‘yan bindiga suka yi ranar Litinin.

Shugaban kungiyar Mr. Sunday Abdu yace kisan mutanen ya auku ne a wurin da sojoji ke gudanar da aikin tsaro a yankin. Yace a dakin da sojoji suka ba mutanen mafaka ne ‘yan bindigan suka shiga suka kashesu. Mr. Abdu yace kowane mako ana kashe masu mutane tare da kone gidajensu. Yace su kam suna ganin dokar hana fita da dare da aka kafa, bata yi tasiri ba.

Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00

Facebook Forum

Bidiyo

Yadda Wani Mutum Ya Mari Shugaban Faransa Emmanuel Macron
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Marigayi TB Joshua
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Gidajen Rediyon Najeriya Sun Gana Da Jami'an Diplomasiyya Kan Rikicin Twitter
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG