Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pompeo Ya Ce Shugaban Amurka Zai Janye Daga Yarjejeniyar Nukiliyar Iran


Mike Pompeo, skataren harkokin wajen Amurka
Mike Pompeo, skataren harkokin wajen Amurka

A ziyarar da yake yi yznzu a gabas ta tsakiya Mike Pompeo sakataren harkokin wajen Amurka ya fada fili Shugaba Trump zai janye dayarjejeniyar nukiliyar da wasu kasashen duniya tare da Amurka suka cimma muddin ba'a yi kwaskwarimar da yake so ba.

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ya fito a fili jiya Lahadi, yace shugaba Donald Trump, yana shirin zai fice daga yarjejeniyar da manyan kasashen duniya tareda Amurkan suka kulla da Iran kan shirin Nukiliyar Farisan, muddin ba'a yiwa yarjejeniyar kwaskwarima ba, idan wa'adin sabunta shirin ya cika cikin watan gobe.

Pompeo, wanda a halin yanzu yake gabas ta tsakiya a ziyararsa ta farko kan wannan mukami a kasashen waje, yace shugaba Trump ya fito fili ya nuna cewa wannan yarjejeniya tana da rauni. Ya umarci jami'an gwamnatinsa suyi aiki domin inganta shi, kuma idan ba za'a yi hakan ba, to zai janye Amurka daga wannan yarjejeniya. Abu ne kai tsaye babu kumbiya kumbiya.

Da yake magana a Isra'ila, Pompeo yace ba kamar sauran gwamnatocin Amurka da suka wuce ba,shugaba Trump yana da ciakken shiri kan Iran, wadda aka tsara da nufin tunkarar jerin barazana da suke fitowa daga hukumomin kasar a Tehran.

A nata bangaren, Iran tace, bata da niyyar canja yarjejeniyar data kulla da kasashen Jamus,da Faransa, da Britaniya, da China da Rasha, da kuma Amurka,ta ko wace hanya ciki harda kulla wata sabuwa.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG