Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Puerto Rico Tana Fama Da Matsaloli Bayan Bala'in Guguwar Maria.


Mazauna Puerto Rico suka yi layi a ATM don fidda kudi

Kimainin rabin al'umar Puerto Rico su milyan 3 da dubu dari hudu,basu da tsabtataccen ruwan sha,da lantarki fiyeda mako daya bayan da guguwar Maria ta afkawa tsibirin.

Mako daya da rabi, bayan da guguwar nan mai tsanani da aka lakabawa suna Maria, ta fatattaki Puerto Rico kimainin rabin al'umar yankin su milyan 3 da dubu dari hudu basu da tsabtataccen ruwan sha, kamar yadda bayanai daga ma'aikatar tsaron Amurka tayi bayani, yayinda kashi 95 cikin dari basu da wutan lantarki.

Duk da haka Gwamnan Puerto Rico Ricardo Rosello ya fada jiya Asabar cewa an samu ci gaba. Yace asibitoci 51 cikin 60 dake yankin suna aiki, yayinda kayan agaji suke isowa ta tashoshin jirgin sama dana ruwa. Hakan nan Gwamnan yace layukan tarho na gida baki daya suna aiki, sai dai hanyoyinsadarwan ba duka bane suke aiki, Gwamna Ricardo yace kashi 33 cikin dari na sadarwa suke aiki.

Gwamna Rosello yace ana share hanyouyin da suke yankin, duk da haka akwai al'umomi da kaiwa inda suke yake da wahala saboda irin barnar da guguwar Maria ta haddasa.
Har yanzu rayuwa a tsibirin yana da wahala inda mutane suke layi a cikin zafin rana mai tsanani domin sayen man fetur, da abinci da kuma fidda kudi.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG