Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Bayyana Ra'ayoyi Kan Sauke Manyan Hafsoshin Sojin Najeriya


Nigeria Police Protest

Bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya biya bukatar 'yan Najeriya na ya sauke manyan hafsoshin sojin kasar, ganin sun kasa kawo karshen Boko Haram da sauran miyagu a fadin kasar.

‘Yan Najeriya sun shiga bayyana ra’ayoyinsu nan da nan bayan sauke manyan hafsoshin sojin Najeriya tare da yin masu ritaya da kuma maye gurbinsu da sabbi. Ra’ayoyin sun kama daga masu nuna cancantar hakan zuwa masu ganin an yi ba a yi ba, ganin cewa an maye gurbin na da ne da wadanda su ma su ka kasa.

Masu takaicin irin hafsoshin da aka nada din, sun yi nuni da yadda su ka kwashe shekaru 11 ba tare da kawo karshen kungiyar Boko Haram ba da kuma sauran matsalolin da aka fuskanta na tsaro, ciki har da na garkuwa da mutane don neman kudin fansa. Shiyyar arewa maso gabashin Najeriya ce ta fi fama da irin wadannan matsalolin.

Kanar Hussaini Manguno (ritaya), mai sharhi kan al’amuran tsaro, ya ce wannan canjin ya dace; ya kara da cewa dama tsoffin sojojin sun tare wuri ma jami’an sojin da ke biye da su. Ya ce an dan yi nasara, duk dayake babu yawa – saboda kimanin kashi 20% na nasara ne kawai aka yi.

Wani dan jahar Borno mai suna Abdullahi Alhassan, ya ce ganin harkar tsaro mashahuriya ce, idan aka lura da yadda ake ta samun matsalar rashin tsaro ciki har da hare haren ‘yan Boko Haram, kamar sam babu ma shugabancin a bangaren tsaro. Ya ce shi kansa Janar Buratai akwai wasu hanyoyin garinsu da bai iya bi.

Shi ma wani mai suna Abubakar Ladan, ya ce lallai Shugaba Buhari ya cancanci yabo, ganin cewa bayan da aka yi ta kururuwan a sauke manyan hafsoshin ya saurari jama’a amma bai gaggauta sauke su ba, sai bayan da ma aka manta. Ya ce ga dukkan alamu wannan canjin zai amfani jama’a.

Ga dai Haruna Dauda da rahotonsa ta sauti:

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG