Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ra’ayin Wasu Akan Labaran Da Suke Ji


Wani mai sauraren Sashen Hausa yana bayyana ra'ayinsa
Wani mai sauraren Sashen Hausa yana bayyana ra'ayinsa

Sashen Hausa ya tara ra’ayoyi daban daban daga masu sauraren gidan rediyon da ma wasu amma dukansu sun yadda Shugaba Buhari mai adalci ne sabanin wadanda ya ba mukami su taya shi rikon amanar da aka ba su

Sashen Hausa ya zagaya cikin wata anuguwa a Birnin Abuja babban Birnin Nigeria domin jin ra’ayin mutane akan labarum da suke ji ko suke karantawa daga kafofin labaru musamman rediyo.

An anguwar Garki Alhassan Idris wanda aka fara tambaya ko ya san inda shugaba Buhari yake sai ya ce ya ji a rediyo ya tafi London domin a sake duba lafiyarsa saboda zaben dake tafe. Ya amince ya je hutu ne amma ya ce yana bukatar a dan dubashi.

Wasu masu sauraren Sashen Hausa
Wasu masu sauraren Sashen Hausa

Alhassan Idris ya manta suna shugaban hukumar DSS da ya rasa mukaminsa kwanaki biyu da suka gabata. Ya ji mataimakin shugaban kasa ya saukar dashi kuma tuni ya maye gurbinsa da wani.

Alhassan ya san cikakken sunanyen ministan shari’a da shugaban jam’iyyar APC. Akan dalilin da ya sa aka kwape shugaban DSS sai ya ce Shugaba Buhari ya daukoshi ya yi aiki amma sai ya kauce hanya yana kasuwanci da mukaminsa. Baicin hakan, a bangaren shugaban kasa abun da ya dace ne shi ya sa suka yi waje dashi.

Shi ko Suleiman Umar bai san sunan ministar kudin Nigeria ba saboda ya watsar da sauraron labarai. Ba ya sauraron duk labarin da ya shafi kudi domin, a cewarsa abubuwa basa tafiya kamar yadda ya taso ya gani. Dalili ke nan da ya dena domin kada ya jawowa kansa hawan jini. A lokacin Sanusi Lamido ya kan saurari labaru.

Abubakar Ibrahim bai san cikakken sunan ministan Abuja ba. Ya ce idan an san sunan mutum yana yiwa mutane adalci ne. Bai san sunan shugaban ma’aikata ba dake fadar shugaba Buhari domin shi ma ba ya yiwa mutane adalci.

A saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya domin karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:53 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG