Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ra'ayoyin Wasu 'Yan Najeriya Kan Cikar Muryar Amurka Shekaru 75 da Kafuwa


A girl with sparkle writes 2020 during the New Year's celebrations in North Macedonia.
A girl with sparkle writes 2020 during the New Year's celebrations in North Macedonia.

Jiya Muryar Amurka tayi bikin cika shekaru saba'in da biyar da kafuwa a birnin Washington, Gundumar Columbia

Wasu 'yan Najeriya da aka nemi ta bikinsu sun bayyana ra'ayoyinsu akan gidan rediyon Muryar Amurka ko VOA.

Dauda Dodo yace akwai shirye-shiryen da Muryar Amurka ta keyi masu kayatarwa da yawa.Yana jin shirye-shiryen bangaren wasanni amma da so samu ne sai a dinga gudanar da shirin na tsawon mintuna goma sha biyar kamar da. Ya so shirin "A Bari Ya Huce" na Ibrahim Alfa. Yace ko bai ji wani labari ba a kodayaushe ya kama Muryar Amurka to ya warke.

Bikin cika shekaru 75
Bikin cika shekaru 75

Malam Yusuf Abubakar a cewarsa duk labarin da aka ji daga Muryar Amurka babu karya ciki saboda sai ta tantace labari kafin ta yada. Akan ko akwai gyara da ya keso a yi, sai malamin yace shi bai ga wani gyara da za'a yi ba domin duk shirye-shiryen sun yi masa.

Shi kuma Malam Aliyu Gwadabe yace Muryar Amurka ke ba talaka dama ya san abun da gwamnati keyi kuma ya kamata tayi. Inji shi talaka bashi da wani gidan rediyo da yake alfahari dashi idan ba Muryar Amurka ba. Yana sha'awar yadda Muryar Amurka ke bin digdigi idan an tauyewa mutum hakkinsa har sai an cimma nasara.

Malam Milari yace tunda yake sauraran radiyon bai taba jin karya ba kamar yadda wasu gidajen rediyo keyi.

Ga raohoton Hassan Umaru Tambuwal da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG