Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ra’ayoyin ‘Yan Nijar Kan Sabuwar Dokar Haraji


Wasu Shugabannin Jamhuriyar Nijar

A kwanan nan ne gwamnatin Nijar ta sanar da wata sabuwar dokar haraji wadda ta hada da biyan haraji kan gida da gado, abun da ‘yan kasar suka ce ba zasu amince ba

Wakiliyar Muryar Amurka, Tamar Abari dake Nijar, ta zagaya ta ji ra’ayoyin mutanen kasar kan sabuwar dokar haraji da kasar ta fitar.

Galibin mutanen da aka yi hira da su duk basu fadi sunayensu ba.

Mace ta farko da ta yi magana kira ta yi ga gwamnatin kasar da ta tausaya wa al’umma ta cire sabon harajin daga kawwunansu, musamman mata, ta dora kan ma’aikata da masu hannu da shuni.

Wani kuma ya ce dokar mai rikitarwa ce kuma wani bakon abu ne aka dauko daga wata kasa ake son a jarabashi a kasarsu. Ya ce suna jiran su ga abun da ‘yan majalisar dokokin kasar zasu yi.

A kan sawa gado haraji kuma, wani dan Nijar cewa yake bai yadda ba tunda akwai tsarin gado a cikin addinin musulunci

Wani ma cewa ya yi abu ne da hankali bai kamata ya dauka ba. Ya ce duk gwamnatocin da aka yi basu kawo irin wannan dokar ba sai ta yanzu.

Ga rahoton Tamar Abari da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG