Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Raila Odinga Ya Kalubalanci Zaben Shugaban Kasar Kenya a Kotun Koli


an takarar shugaban kasar Kenya Raila Odinga
Dan takarar shugaban kasar Kenya da ya sha kaye, ya shigar da kara kotu yana kalubalantar sakamakon zaben da aka gudanar makon jiya.

Raila Odinga ya shigar da karar ne a kotun kolin kasar dake birnin Nairobi yau asabar.

Tun farko yau asabar da safe ‘yan sanda suka yi amfani da barkonon tsohuwa domin tarwatsa wani gungun jama’a da suka taru a Nairobi domin goyon bayan Mr. Odinga Firai Minista mai barin gado.

Jam’iyarsa ta Coaliation for Reform and Democracy-CORD ta bayyana kwarin guiwa cewa Mr. Odinga zai yi nasara a kotu.

Mr. Odinga yaki amincewa da sakamakon zaben da aka gudanar bisa zargin cewa an tafka magudi a kirga kuri’un.

Hukumar zabe ta bayyana Uhuru Kenyatta a matsayin wanda ya lashe zabe inda ya sami kashi 50.7% na kuri’un, ya kuma sami rinjayen da ya zama ba a bukatar zuwa zagayen zabe na biyu.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG