Dubban ma'aikata a fadin duniya sun yi maci kan tituna asabar din nan a Ranar Ma'aikata Ta Duniya, su na neman da a kyautata irin albashin da ake biyansu da kuma yanayin aikinsu.
A Istanbul a Turkiyya a karon farko cikin shekaru 30, an kyale ma'aikata sun yi gangami cikin dandalin Taksim dake tsakiyar birnin, domin karrama wannan rana. An takaita yin taro a wannan dandali tun shekarar 1977 a lokacin da wasu 'yan bindigar da ba a san ko su wanene ba suka bude wuta a kan masu zanga-zanga a dandalin, suka haddasa ture-ture wajen enman tserewa tare da mutuwar mutane fiye da 30.
A birnin moscow, dubban 'yan Kwaminis sun yi maci dauke da jajayen tuta da hotunan Josef Stalin, a wani bukin da yayi kama da irin wanda aka saba gani a zamanin tsohuwar Tarayyar Soviet. A wani gangamin na dabam, madugun 'yan hamayya Garry Kasparov, ya jagoranci wasu daruruwan mutane wajen yin tur da firayim ministan Rasha, Vladimir Putin.
A kasar Pakistan, firayim minista Yousuf Raza Gilani ya karrama wannan rana ta hanyar bayar da sanarwar karin Dalar Amurka 12 (kimanin naira dubu daya da dari takwas) a kan albashi mafi kankanci da za a iya biyan ma'aikaci a kasar. A yanzu albashi mafi kankanci a wata zai koma Dalar Amurka 83 (kimanin Naira dubu 12 da 600).
Firayim ministan na Pakistan ya ce wannan sabon tsarin albashi zai taimakawa ma'aikata miliyan 50.