Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Tunawa Da Matan Da Suka Rasa Mazajensu A Duniya


Mata Da Suka Rasa Mazajensu A Sansanin Damare
Mata Da Suka Rasa Mazajensu A Sansanin Damare

Yayin da yau duniya ke juyayi makomar matan da suka rasa mazajensu da irin halin rayuwa da suka sami kansu a ciki, akwai irin wadannan mata zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira da baya ga asarar mazansu, sun rasa ‘ya’yansu da duk abinda suka mallaka sakamakon rikicin Boko Haram.

Wasu mata da Muryar Amurka ta yi hira da su kamar su Gambo Suleiman, A’isha Ali da Sutu Nuhu, sun ce mazansu sun bar su da dawainiyar renon yara ga shi kuma babu taimakon da suke samu daga ‘yan uwa ko dangin mazan nasu. Akwai kuma matsalar kyama da talauci da suke fama da su.

Kimani wadannan mata da yara sama da miliyan dari biyu ne, a cewar wasu bayanai da majalisar dinkin duniya ta fitar na bana mai taken ‘Kauda Zaman Kadaici’ na ranar tunawa da matan da suka rasa mazajensu. Mafi yawansu na zaune nahiyar Afrika da Indiya ne ke rayuwa a wani hali mai ban takaici.

A cikin wannan rahoton, wakilinmu Sanusi Adamu ya yi nazarin halin rayuwa da rukunin na wadanan mata suka fada a ciki a sansanin ‘ya gudun hijira na Damare dake jihar Adamawa, ayi sauraro lafiya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG