Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rarrabuwar kawuna Tsakanin Kabilun Yemel, Yana kara Iza Wutar Rikicin Kasar


Wani mai goyon bayan shugaban kabilar Hashid Shiekh Sadeq al-Ahmar,da aka jikkata ake nemawa jinya.

Jami’an tsaron Yemen da magoya bayan shugaban wata kabila sun kara a wajajen fitar birnin Sana’a, fadar kasar.

Jami’an tsaron Yemen da magoya bayan shugaban wata kabila sun kara a wajajen fitar birnin Sana’a, fadar kasar.

Shaidu suka ce daruruwan magoya bayan Sheikh Sadeq al-Ahmar, suna kokarin kaiwa ga unguwar Hasaba dake Sana’a, inda shugaban yake da zama, tuni dakarun gwamnati suke fatattakar unguwar. Sunce an kashe mutane da dama a fadan da ake yi.

Lamarin yasa an tsaida zirga zirgan jiragen sama a tashar jirage a Sana’a babban birnin kasar, sakamakon zafafa fada tsakanin dakarun gwamnati da kabilun,kuma fadan ya kai kusa da tashar.

Sojojin gwamnati sun bude wuta kan masu zanga zangar neman kawo Karshen mulkin shugaba Ali Abdullah Sale. ‘Yan gwagwarmaya sunce an kashe akalla mutane ashirin da biyar a fadace fadace da ake yi a yankin cikin ‘yan kwanaki da suka wuce.

Rikicin na Yemen ya sa wasu kasashe rage yawan jami’an jakadancinsu a kasar,ko kuma su rufe ofisoshinsu baki daya.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG