Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Da Iran Na Nuna Kadara A Fadan Syria


Jirgin yakin Rasha a Syria

Amfani da wani sansanin kasar Iran wajen kaddamar da harin sararin sama da Rasha tayi, ya tada hankalin Amurka da abokan kawancenta a yankin, sai dai an fi bayyana damuwa dangane da makomar gwamnatin Syria fiye da nuna gadara da Moscow ko Tehran ke yi.

Rasha da Iran suna kara kidima, ganin yadda ‘yan tawaye suke kara matsawa dakarun gwamnatin Syria lamba a kudanci da kuma gabashin kasar, da hari na baya bayan nan da suka kai a birnin Aleppo.

Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta bayyana jiya Talata cewa, jiragen saman yaki samfanin Tu-22M3 da Su-34 sun tashi daga sasanin mayakan saman Iran Hamedan domin kaiwa mayakan ISIS da kuma na alqaida hari da ake alakantawa da kungiyar Jabhat al Nusra a Aleppo da kuma Deir ex-Zor Idlib, bisa ga cewar ma’aikatar,

Duk da haka, sai kace hare haren da Rasha ke kaiwa, yunkuri ne na karawa dakarun dake tare da shugaban Syria Bashar al-Assad karfi.

Galibin tallafin yana zuwa ne ta kasa, inda ake ganin alamun kwararar mayakan da Iran ke marawa baya.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG