Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Da Jahar Bauchi Sun Rattaba Hannu Kan Hakar Mai Da Iskar Gas


Hedikwatar kamfanin man Najeriya, NNPC da ke Abuja
Hedikwatar kamfanin man Najeriya, NNPC da ke Abuja

A wani cigaba a kokarin da ake na samun mai a arewacin Najeriya, jahar Bauci da wani kamfanin hako ma'adinai na kasar Rasha na shirin hako mai a Baucin.

Gwamnatin jahar Bauci da wani kamfanin hakar mai da ke kasar Rasha sun rattaba hannu kan wata yarjajjeniyar kasuwanci ta hako mai da iskar gas a jahar Bauci. Wannan, a cewar wakilinmu a Bauci Abdulwahab Muhammad, ya zo daidai na shelar da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi na ba da himma wajen harkar hako albarkatun mai a arewacin Najeriya.

Hakazalika, gwamnan jahar Bauchi, Alhaji Mohammed Abdullahi Abubakar, y ace za a rinka karbar haraji kan duk masu hakar ma’adinai a jahar, wanda don haka ne ma aka bullo da wata sabuwar doka. Y ace da zarar an kaddamar da dokar za a cigaba da karbar haraji da kuma harkokin hakar ma’adinai gadan-gadan.

Gwamnan na jahar Bauci y ace kamfanin hakar ma’adinan na kasar Rasha na daya daga cikin kamfanonin da su ka shaharar a harkar ma’adinai a duniya, wanda ya tabbatar da kasancewar mai a arewacin Najeriya – musamman ma Bauchi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:03 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG