Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Bata Amince Da Hukuncin Da Kwamitin Olypmpics Ya Yanke Mata Ba


Russia Olympics

An yanke shawarar hana Rasha shiga wasannin kasa da kasa a matsayin kasa, sai dai 'yan wasan kasar su na iya shiga cikin wannan gasar wasannin Olympics na hunturu da za a yi a Koriya ta Kudu.

Kasar Rasha tace tana bukatar ta yi nazarin hukuncin da kwamitin gasar wasannin Olympics na kasa-da-kasa da ake kira IOC a takaice ya dauka na hana kasar ta Rasha shiga gasar wasannin motsa jiki na Olympics na hunturu wanda za a yi a Pyeongchang dake Korea ta kudu kafin ta dauki wasu matakai.

Mai Magana da yawun fadar shugaban Rasha Dmitry Pescov ya fadawa manema labarai a yau laraba cewa muhimmin abu a yanzu shine kare hakkokin ‘yan wasan Rasha.

Kwamitin na IOC ya yanke hukunci jiya Talata cewa ‘yan Rasha zasu iya shiga gasar a matsayin ‘yan wasa daga Rasha amma ba a matsayin kasa ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG