Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha: Kotu Ta Samu Navalny Da Laifin Almubazzaranci


Wani Alkali a Rasha ya yanke hukunci dake nuna cewa an samu Shugaban 'yan adawa, Alexei Navalny, da laifin yin almubazzaranci, matakin da watakila ka iya kawo mai cikas a kokarin da ya ke yi na tsayawa takarar shugabancin kasar da za a yi a shekara mai zuwa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Interfax ya bayyana.

Su dai masu shigar da kara sun nemi da a yanke mai hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru biyar

Kamfanin Dillancin Labaran na Interfax ya ruwaito wani Lauyan Navalny ya na cewa hukuncin zai iya hana shi takarar zaben shugabancin kasar.

Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin bai bayyana ko zai sake tsayawa takarar kujerarsa ba.

Navalny ya fito idon duniya ne bayan da ya fallasa almundahanar da ake yi a wasu ma'aikatun gwamnatin kasar.

Shi ne kuma ya jagoranci zanga zanga a shekarun 2011 da kuma 2012 wacce ta hade kai wajen kalubalantar dawowar Putin kan karagar mulki.

Navalny ya ce zai ci gaba da harkokin siyasarsa duk da hukuncinsa da aka yanke masa.

XS
SM
MD
LG