Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

RASHA: Mutane 10 Suka Halaka A Sanadiyar Fashewar Wani Abu A Tashar Jirgin Kasa


Tashar da wani abu kaman bam ya fashe a birnin St. Petersburg
Tashar da wani abu kaman bam ya fashe a birnin St. Petersburg

Hukumomi a Rasha sun ce akalla mutane goma aka kashe, wasu hamsin kuma suka jikata a cikin wata pashewa a tashar jirgin kasa a birnin St. Petersburg.

Kafofin yada labarai a Rasha sun ruwaito cewar fashewar ta auku ne a tashar jirgin dake Sannaya Square a tsakiyar birnin.

A halin yanzu an rufe duka tashoshin jirgin kasa dake cikin birni mafi girma na biyu a kasara Rasha.

Kawo yanzu, ba a gano sanadiyar fashewar ba, amma shugaban Rasha Vladmir Putin ya ce bincike zai duba kowane fanni har da ayyukan ta’addanci.

Yace har iyau dalilan wannan fashewar basu bayyana ba a daidai wannan lokaci da faruwar abin.

Putin ya isa St. Petersburg a yau Litinin don gudanar da jawabinsa na shekara-shekara ga manema labarai wanda kungiyar siyasar mai samun goyon bayan kasar ta Kremlin ke shiryawa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG