Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Na Baiwa Ukraine Shawara


Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergei Lavrov
Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergei Lavrov

​Sakataren Harkokin Wajen Rasha Sergei Lavrov ya ba da shawarar a tattauna tsakanin gwamnatin Ukraine da 'yan aware magoya bayan Rasha da ke kudu maso gabashin Ukraine.

Lavrov yace "Rasha ta yi imanin cewa ana iya tattaunawa tsakanin hukumomin da ke Kyiv da 'yan adawa, ko kuma a shirya ta karkashin laimar Kungiyar Hadin Kan Tabbatar Da Tsaro a Turai. Mu na fatan dai abokanmu, takwarorinmu na Yammacin duniya za su bar Ukraine ta shirya tattaunawar ba tare da wani tarnaki ba."

Firayim Ministan ya yi wannan maganar ce a yayin ziyarar da ya kai Peru.

A gabashin Ukraine, hukumomin yankin sun fadi jiya Laraba cewa wasu 'yan bindiga magoya bayan Rasha sun kame wani ginin majalisar birnin Horlivka, wanda birni ne mai yawan mutane 290,000 da ke arewacin birnin hada-hadar kasuwanci na Donetsk.

A yanzu 'yan aware na rike da birane da dama a gabashin Ukraine mai cike da masana'antu, ciki har da Donetsk, inda 'yan tawayen su ka tsaida ran 11 ga watan Mayu a zaman ranar gudanar da zaben raba gardama kan zancen ballewa daga Ukraine.

Kuri'a makamanciyar wannan da aka kada a watan jiya ta kai ga hadewar tsibirin Crimea da Rasha.

Shugaban wuccin gadin Ukraine Oleksandr Turchynov ya ce gwamnatinsa ta kasa shawo kan yawaitar 'yan aware magoya bayan Rasha a yankuna biyu na gabashin Ukraine kuma ba za ta iya shawo kan sojojinta ba.
XS
SM
MD
LG