Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Ta Kalubalanci Kasancewar Turkiyya a Syria


Shugaban Rasha, Vladimir Putin a wani taro da dakarun kasar kan batun Syria
Shugaban Rasha, Vladimir Putin a wani taro da dakarun kasar kan batun Syria

Rasha ta ce ta ji takaicin kin amincewa da aka yi da kudirin da ta gabatarwa Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya nemi Turkiyya ta kawo karshen ayyukan sojinta a Syria.

A yau Asabar Fadar Kremlin ta fitar da wata sanarwa, tana mai jaddada aniyarta, ta ganin an tabbatar da zaman lafiya, ta hanyar kawar da ‘yan ta’adda, wanda hakan a cewarta zai kawar ‘yan ta’adda kasar ta Syria.

A jiya juma’a, Amurka da Rasha suka kaddamar da wata tattaunawa kan yadda za a cimma matsayar tsagaita wuta a kasar ta Syria.

Jami’an gwamnatocin biyu, sun tattauna ne a Geneva domin samar da hanyar da za a samu dogon lokaci na tsagaita wuta, saboda akai kayan agaji ga yankunan da aka yiwa kawanya.

Kasashe 17 da ke marawa gwamnatin Syria baya, sun amince da kafa wani kwamiti da zai maida hankali wajen ganin an cimma matsayar tsagaita wutar a karkashin kulawar Majalisar Dinmkin Duniya, a taron da suka yi a Munich, inda aka nada Amurka da Rasha a matsayin wadanda za su jagorancin tafiyar.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG