Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar 'Yan Jaridar Kasa Da Kasa Ta Yi Tir Da Karyar Mutuwar Dan Jarida Arkady


Jami'an Tsaro Da 'yan Jarida
Jami'an Tsaro Da 'yan Jarida

Wani mai magana da yawun fadar gwamnatin kasar Rasha ya fada yau Alhamis 31 ga watan nan na Mayu cewa, Rasha ta yi murna da jin dan jarida Arkady Babchenko na raye, amma kuma labarin mutuwarsa na jabu abin mamaki.

An sami rahoton harbin sanannen dan jaridar nan Arkady Babchen mai bada rahotanni akan yaki kuma mai sukar gwamnatin Kremlin a ranar Talatar da ta wuce a matattakalar benen gidansa da ke birnin Kyiv.

Amma sai kuma ga Bobchenko ya ba ‘yan jarida mamaki a lokacin daya bayyana lami lafiya a jiya Laraba, yayin da jami’an tsaron Ukraine suka bayyana labarin mutuwarsa a matsayin na jabu ne don a ceci rayuwar dan jaridar.

Mai magana da yawun fadar Kremlin, Dmitry Peskov ya fada yau Alhamis cewa bai san ko sakamakon wannan matakin ya cancanta ba, kuma abinda ya faru bai canza yadda Rasha ke kallon Ukraine a matsayin kasa mafi muni ga ‘yan jarida ba.

Kungiyar da ke kare ‘yan jarida ta kasa-da-kasa ta yi Allah Wadai da labarin mutuwar Bobchenko na karya, tana mai cewa “abin tada hankali ne, na da-na-sani kuma” ya kara da cewa dakarun tsaron Ukraine suna wasa da gaskiya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG