Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Ta Yi Watsi Da Rahoton Jaridar New York Times


Vladimir Putin

kasar Rasha ta yi watsi da rahoton da jaridar New York Times ta buga wanda ya ce wasu daga cikin wadanda suka yiwa shugaba Donald Trump kamfe da wasu da suka yi masa hidima sun tuntubi wasu manyan jami’an leken asirin Rasha a lokuta da dama kafin zaben da aka yi cikin watan Nuwamban bara.

Jaridar ta ambaci wasu jami’an gwamnatin Amurka hudu, na yanzu da na baya suna cewa hukumomin leken asiri da na kiyaye doka da oda sun sami hirar waya da kuma wasu kiraye-kirayen waya da aka yi wadanda suka hada da manajan kamfe din Trump a lokacin Paul Manafort da wasu mukarrabansa da ba a bayyana sunayensu ba.

Sai dai Manafort ya ce wannan zance ne mara tushe, a cewar jaridar ta New York Times.

Haka kuma ya musanta makamancin wannan rahoton da gidan talabijin din CNN ya bada na cewa, masu yiwa Trump hidima, ciki har da Manafort din da mai ba shugaba Donald Trump shawara ta fannin tsaro da yai murabus a ranar Litinin din da ta gabata, Michael Flynn da wasu da yawa da ba a bayyana sunayensu ba sun yi ta ganawa da jami’an Rasha kafin zaben.

Yau laraba a Moscow, kakakin fadar Kremlin, Dmitry Peskov, ya ce wannan rahoton ba a gina shi bisa hujja ta zahiri ba.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG