Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Farashi Daya Na Kudaden Waje Ya Hana Tattalin Arzikin Najeriya Farfadowa


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari dake kokarin farfado da tattalin arzikin kasar
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari dake kokarin farfado da tattalin arzikin kasar

A daidai lokacin da Najeriya ke daukan matakan farfadowa da tattalin arzikinta wasu kwararru sun yi tsokaci akan matsalolin da suka hana kasar cigaba ta fannin farfado da tattalin arziki.

Kwararrun na ganin cewa farashi daban daban na kudaden kasashen waje tsakanin hudu zuwa biyar wanda shi ne irinsa na farko a duk duniya sabanin a ce akwai farashi daya da kasar zata yi anfani dashi.

Malam Ahmed Yusuf tsohon babban daraktan Unity Bank yace babu shakka samun farashin dala wajen guda hudu shi ne gimshikin abun da ya sa Najeriya ta kasa fita daga kangin tabarbarewar tattalin arziki. Yace kokarin da gwamnati ta keyi domin taimakawa wasu ya sa suka kirkiro da farashi da yawa.

Inji Malam Yusuf akwai banbancin farashin da bankuna ke anfani dashi. Haka ma akwai farashin da babban banki ke ba kankuna wanda ya sha banban da wanda take ba masu shigo da kaya daga kasashen waje. Akwai farashin da ake ba masu shigo da man fetur. Akwai kuma farashin bayan fagge.

Farashi barkatai haka babu tsari ba daidai ba ne inji Malam Yusuf. Misali yace babu tabbas wanda aka sayarwa kudin waje ta wata hanya mai sauki ba zai juya ya je inda kudin ke da tsada ba ya sayar.

Malam Yusuf ya cigaba da bada misali da masu musayar kudi. Yace su bai kamata a ce suna sayar da miliyoyi ba domin tamkar 'yan kwamisho ne.

Ga rahoton Umar Musa Faruk da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:48 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG