Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Kudaden Tallafi Zai Janyo Asarar Rayuka A Yemen


Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci wadanda suka yi alkawarin bada tallafin kudade domin taimakawa mutanen kasar Yemen da suke fuskantar yunwa su cika alkawuran da su ka yi.

Harkokin Majalisar Dinkin Duniya a kasar Yemen na fuskantar karancin kudi, kuma dole kwanan nan a rage adadin kayan abincin da ake bai wa mutane miliyan 12, a kuma kawo karshen wasu ayyukan ceto, muddun masu bayar da gudunmowa ba su cika alkawuransu ba.

“Mun zaku mu samu kudaden da aka mana alkawari,” a cewar Lise Grande, shugabar shirye-shiryen Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Yemen, a wata takardar bayani a jiya Laraba. Ta kara da cewa, “Muddun kudi bai zo ba, mutuwa mutane za su yi.”

Wannan shekarar, daga cikin shirye-shiryen Majalisar Dinkin Duniya 34 da ake yi a kasar ta Yemen, guda uku ne kadai aka samar da kudin gudanar da su.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG