Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rashin Nasara Bai Karya Gwiwar Bernie Sanders Ba


Bernie Sanders

Sanata Bernie Sanders na jihar Vermont ta Amurka ya fada cewa zai ci gaba da yakin neman zaman dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Democrat, duk kuwa da cewa ya tabbatar da cewa yana dada rasa masu kada masa kuri’a.

'Yan jam'iyyar tasu dai wadanda ke dada komawa ga tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden, bisa tambayar da ake ta yi kan cewa wanene daga cikinsu ake ganin zai iya kayar da shugaban kasa Donald Trump na jam’iyyar Republican a babban zaben da za a gudanar a watan Nuwamba.

“Abu ne karara cewa wannan ba rana bace mai kyau ga kamfen dina” a cewar Sanders kan zaben fidda dan takara na jihohi shida da aka yi ranar Talata.

A zaben dai Biden ne ya lashe hudu daga cikin jihohin, ciki har da jihar Michigan mai wakilan daligate mai yawa.

Sanders wanda ke ayyana kansa a matsayin mai ra’ayin gurguzu, ya ce yana jiran lokacin da zai yi muhawara da Biden.

Wannan dai shi ne karo na uku da yake neman tsayawa takarar shugaban kasa cikin shekaru 30.

Facebook Forum

Rayuwar Birni

Rayuwar Birni – Dan Kasuwar Gwari A Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00
Karin bayani akan Rayuwar Birni

Arewa A Yau

Arewa A Yau
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:00:47 0:00
XS
SM
MD
LG