Jami'an tsaro, tare da goyon bayan gwamnatin jihar Borno, sun gudanar da taron fadakar da shugabannin addinin Islama da Kiristanci.
A wurin taron gwamnan jihar, wanda kwamishanan shari'ar jihar Barrister Kaka Shehu Lawal ya wakilta, ya ce rashin sani da jahilci da talauci ke jefa matasa cikin ayyukan ta'addanci.
A cewar kwamishanan, gwamnatin jihar ta shirya ta taimaki matasan jihar.
Da yake zantawa da wakilinmu, Barrister Lawal yace an fara samun zaman lafiya saboda haka jami'an tsaro suka ga ya kamata a zauna da malaman addini da sarakuna domin a samu fahimtar juna dangane da yadda za’a taimakawa matasa don su daina kauce hanya duk da matsalolin talauchi da jahilci da suke fuskanta.
Ga Haruna Dauda da karin bayani.
Facebook Forum